Babu shakka ziyarar da mataimakin firaministan kasar Sin ya kai a kasashen Saudia da Iran, wani muhimmin aiki ne gwamnatin jamhuriyar jama'ar Sin suke yi wajen ganin kasashen Iran da Saudia sun kawo karshen mujadala da rashin jutuwa dake wanzuwa a tsakanin kasashen 2 ta yadda kasashen za su maida da huldar jakadanci da diplomasiyya a tsakaninsu. Hakika wannan aniya ce mai kyau kasar Sin suka dauka da zummar kawo karshen rashin fahimtar juna tsakan Tehran da Riyad na kasar Saudi-arebia. Agaskiya, mahukuntan kasar Sin sun yi dogon tunani da hangen nesa da suka yanke shawarar samar da daidaito tsakanin kasashen Iran da Saudi-arebia wayanda ke tada jijiyoyin wuya sakamakon wata baraka da ta kunnu kai a tsakanin kasashen Saudia da Iran. Ina fata sauran kasashen duniya takwarorin kasar Sin za su hanzarta yin koyi da mahukuntan kasar Sin wajen dakile ruruwar wutar rikici dake ci gaba da ci bal!bal!! Tsakanin Iran da Saudia.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.