Babu shakka, kasar Sin sun cancanci babban yabo bisa kokarinsu na ingiza zaman lafiya a dud duniya. Bayanda kasashen Saudia da Iran suka katse huldar jakanci da junansu bisa dalilan hukuncin kisa da mahukuntan kasar Saudia suka aiwatar akan wani babban malami mai bin mazahabar shi'a. A lokacin da kasashen 2 wata Saudia da Iran suke cece-kuce tare da yanke huldar jakandanci da junansu, kasar Sin ta maida hankali sosai wajen ganin kasashen Iran da Saudia sun samu daidaito a tsakaninsu ta yadda kasashen 2 zasu ci gaba da yin mu'amula da juna kamar yadda suka saba. Agaskiya, ni mahukuntan kasar Sin sun yi tunani da hangen nesa mai kyau da suka yanke shawarar shiga tsakanin dan samar da mafita da zaman karko a tsakanin kasar Saudia da kasar Iran.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.