in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Allah Daya Gari Bambam na farko a sabuwar shekarar miladiyya ta 2016
2016-01-02 12:13:33 cri

A ranar juma'a 01 ga watan Janairu, 2016, muka samu zarafin sauraron shirin 'Allah Daya Gari Bambam' wanda malam Mamman Ada da malama Lubabatu suka gabatar mana. Agaskiya na ji dadin yadda suka gabatar mana da shirin inda Malamai Mamman Ada da Lubabatu suka gabatar mana da muhimman abubuwan da suka faru a shekarar bara(2015) a kasar Sin da kasashenmu na Afirka da ma dud duniya inda suka yi tsokaci adangane da bikin tunawa da yakin Japanawa da kasar Sin(war of resistance) da kuma batun kai harin ta'addanci a birnin Paris na kasar Faransa kana malaman wato, Mamman Ada da Lubabatu sun tabo batun rittaba hannu adangane da harkokin sifiri da masana'antu da taron hadin gwiwar Sin da Afirka(focac) da kuma nasarar gudanar da zabukan gama-gari da aka yi a kasashen taraiyar Nigeria da dai sauran kasashe. Amma, ni nafi sha'awar tsokacin da malaman suka yi adangane da batun nasarar samun nasarar zaben gama-gari da aka yi a taraiyar Nigeria da taron hadin gwiwar kasar Sin da Afirka a karon farko a kasar Afirka ta kudu inda kasar Sin da aminanta kasashenmu na Afirka suka daddale muhimman shawarwari tare da rittabata hannu bisa matakan bunkasa harkokin sifiri da kasuwanci da kuma kara kyautatuwar cin moriyar juna bisa manyan tsare-tsare bisa dukkan matakan samun bunkasuwa a sabbin salon samun bunkasuwa a tsakanin kasashenmu na Afirka da Sin. Barka da shigowar sabuwar shekarar miladiyya ta 2016, zuwa ga dukkan ma'aikatan sashin Hausa na Radiyo kasar Sin tare da fatan za ku kara matsa kaimi wajen watso mana da labarun duniya da ratsin rahotanni da sauran shirye-shiryenku masu farin jini da ilmantarwa ga mu masu sauraro a cikin sabuwar shekarar 2016 da muka shiga, amin.

Daga Alhaji Ali kiraji Gashua, shugaban masu sauraron Cri Hausa na jihar Yobe, taraiyar Nigeria.

Xie xie.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China