Slm. Yanzu muna maida hankali ga ziyarar da shugaban kasar Sin mr. Xi Jinping ya fara a kasar Turkey domun halartar taron G20 a kasar Turkiya da kuma taron Asia Pacific Economic Cooperation(apec) mr. Zai gana da wasu shugabannin kasashen BRICS inda ake sa ran mr. Xi zai tabo muhimman batutuwan da suka jibanci tattalin arziki da dai sauransu. A ranakun 18-19 ga watan Nuwamba, 2015 mr. Xi zai halarcin taron kasashen APEC. Wannan taruka da mr. Xi zai gabatar da jawabai, zai kara wa kasashen su samu bunkasuwa a cikin kankanin lokaci kuma a cikin hanzari. A matsayin kasar Sin kasa ta 2 a dud duniya wajen karfin tattalin arziki, kasar Sin ka iya bada babbar gudumowar ga tarukan G20 da kkuma na kasashen Asia Pacific Economic cooperation da kuma ganawar mr. Xi da wasu shugabannin kasashen BRICs, ka iya kawo babban moriya ga kasashen duniya, masamman kasashenmu na Afirka masu tasowa.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.