Tare da fatan baki dayan ma'aikatan ku suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing. Ra'ayina dangane da taro na 5 na kwamitin tsakiya na JKS wanda aka kammala a karshen watan Oktoban da ya gabata, inda wakilan suka zartar da shirin bunkasa tattalin arzikin kasa na shekaru biyar biyar karo na 13.
Hakika, tsarin mulkin kasar Sin da ya tanadi gabatar da wannan shiri na bunkasa tattalin arziki bayan kowanne shekaru biyar ya burge ni matuka, domin akwai hikimar gaske wajen kirkiro wannan shiri da ke aiwatar da gyaran fuska ga tsarin tattalin arziki da kuma sauran manufofin gwamnati dsa suka shafi raya tattalin arzikin kasa da suka dace da yanayin da ake ciki.
Fata na ga kasar Sin cikin shekaru 5 masu zuwa shi ne, samun nasarar cimma kudurori da manufofin da aka tsara wanda suka hada da rage fadin gibin da ke tsakanin masu iko da kuma masu karamin karfi wato samar da daidaito tsakanin al'umma, da tsimin makamashi, da bayar da muhimmanci ga makamashi mai tsafta wanda ba shi da wata barazana ga muhalli da kuma kokarin bunkasa kirkire kirkire. Ko shakka babu, wadannan burika da kasar Sin ta sanya a gaba sun dace da bukatar zamanin da ake ciki kuma za su taimaka wa kasar Sin tunkarar matsalar tafiyar wahainiya da tattalin arzikin duniya ya samu kansa a ciki.
Kamar yadda ta riga ta bayyana ga kowa, kasar Sin ta riga ta bude hannuwanta kuma ta rungumi kasashe masu tasowaq musamman na nahiyar mu Afirka, don haka, yana daga cikin fata na ganin bunkasar tattalin arzikin kasar Sin ya dore ba wai nan da shekaru 5 kawai ba har ma na dogon lokaci, domin suma kasashen na Afirka su ci gaba da cin gajiyar wannan dimbin arziki da kasar Sin ta mallaka.
Mai sauraron ku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Great Wall CRI Listeners' Club
Kanon Dabo, Nigeria