logo

HAUSA

Xi ya jaddada inganta yin gyare-gyare a taron nazari na manyan jami’ai

2024-10-29 20:29:20 CMG Hausa

A yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da a hada karfi da karfe don ciyar da sauye-sauye gaba cikin kwanciyar hankali da dorewa, yayin da yake gabatar da jawabi ga manyan jami’ai dake halartar taron nazari na babbar makarantar koyon ilmin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin.

Xi ya bayyana hakan ne a lokacin bude taron nazari a babbar makarantar koyon ilmin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato kwalejin gudanar da ayyukan shugabanci ta kasa, ga manyan jami’ai a matakin lardi da na ministoci.

Taron dai an yi shi ne kan aiwatar da tsare-tsare na cikakken zaman taro na uku na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20, wanda ya fitar da sabon tsarin yin gyare-gyare ga kasar. (Yahaya)