logo

HAUSA

An kaddamar da ginin masana’antar kera motoci masu tashi mafi girma a duniya a lardin Guangdong na kasar Sin

2024-10-28 14:23:54 CMG Hausa

An kaddamar da ginin masana’antar kera motoci masu tashi sama mafi girma a duniya, a birnin Guangzhou na lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin.

A jiya Lahadi ne kamfanin XPENG AEROHT, wanda bangare ne na kamfanin XPENG mai kera motoci masu aiki da lantarki ya kaddamar da ginin masana’antar, wadda ita ce irinta ta farko a duniya, da za ta rika samar da adadi mai yawa na motoci masu tashi domin biyan bukatun al’umma.

Rahotanni daga XPENG AEROHT, na cewa zangon farko na aikin ginin kamfanin, zai gudana ne a wuri mai fadin hekta 18, za kuma a yi amfani da shi wajen tsara samfurin mota mai zirga-zirga a sama, inda ake fatan rika kera 10,000 a duk shekara.

A cewar mamallakin kamfanin XPENG AEROHT Zhao Deli, mota mai tashi da kamfanin ya kera, aka kuma kammala gwajinta a watan Satumba, za ta shiga tsarin sayarwa masu bukata a karshen shekarar nan. (Saminu Alhassan)