Shugaban kasar Finland zai ziyarci kasar Sin
2024-10-26 16:08:33 CMG Hausa
Bisa gayyatar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi masa, shugaban kasar Finland Alexander Stubb, zai gudanar da ziyarar aiki a kasar Sin, tun daga ranar Litinin 28 ga watan nan zuwa Alhamis 31 ga wata, kamar dai yadda kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a jiya Juma’a. (Saminu Alhassan)