Xi Jinping ya gana da shugabannin kasa da kasa a Kazan na Rasha
2024-10-23 11:11:19 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, a Kazan na kasar Rasha da yammacin jiya Talata. Xi ya jadadda cewa, yanzu duniya na fuskantar sauye-sauye da ba a taba ganin irinsu ba a cikin karnin da ya gabata. Ana fama da mabambantan rikice-rikice. Duk da haka, daddaden huldar Sin da Rasha na kara karuwa, nauyin da ke wuyansu na amfanawa al’ummar duniya ba zai canja ba.
Xi ya kuma nanata cewa, badi ta cika shekaru 80 da kafuwar MDD, kuma ta cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin kin bin tafarkin murdiya. A matsayin wakilai dindindin na kwamitin sulhu na MDD, kana kasashe daga cikin kasashe mafi karfin tattalin arziki a duniya, kamata ya yi Sin da Rasha su nace ga ra’ayi mai dacewa kan yakin duniya na biyu, da ma nacewa ga tsarin duniya bisa tushen MDD ba tare da canjawa ba, tare kuma da kare dorewar tsare-tsaren duniya cikin hadin kai, da ma kiyaye adalci da daidaici a duniya. Xi ya ce, tsarin BRICS ya kasance wani muhimmin dandali ne ga hadin gwiwar kasashe masu saurin bunkasuwa da masu tasowa a duniya. Sin na jinjinawa rawar da Rasha take takawa ga taron shugabannin BRICS.
A nasa bangare, Putin ya ce, yana fatan kara cudanya na manyan shugabannin kasashen biyu a harkokin kasa da kasa da zurfafa yin mu’ammala kan manyan tsare-tsare, da kuma kiyaye adalci da daidaici da tsarin duniya mai dorewa cikin hadin kai.
Kazalika, a daren wannan rana, Xi Jinping ya gana da babban sakantaren jam’iyyar LPRP, kana shugaban kasar Laos Thongloun Sisoulith. (Amina Xu)