Sama da kungiyoyin agaji 15,000 ne suka yi rajista a kasar Sin
2024-10-23 20:04:46 CMG Hausa
Ma’aikatar lura da harkokin al’umma ta kasar Sin, ta ce sama da kungiyoyin agaji 15,000 ne suka yi rajista a kasar, adadin da ya ninka sau 3 kan na shekaru 5 da suka gabata.
Ma’aikatar ta bayyana hakan ne a Larabar nan, yayin wani taron manema labarai da aka gudanar, inda ta ce jimillar irin wadannan kungiyoyi 2,062 sun yi rajista ne da sassan gwamnati, adadin da ya ninka na shekaru 5 da suka shude har sau 15.
Ma’aikatar ta kara da cewa, daga shekarar 2018 zuwa 2020, wato lokaci mafi muhimmanci na gangamin yaki da fatara na kasar Sin, irin wadannan kungiyoyi na ba da agaji, sun kashe kudade da yawan su ya kai kimanin yuan biliyan 50, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 7 a fannonin da suka shafi yaki da fatara, musamman bangaren tallafawa jama’a dake cikin matsanancin talauci, a yankunan kasar masu rangwamen ci gaba. (Saminu Alhassan)