Kwararrun Zambia: BRICS na matsayin muhimmin tsari na tattalin arzikin kasashe masu saurin ci gaban tattalin arziki
2024-10-23 11:31:30 CMG Hausa
Yayin da aka fara gudanar da taron kolin BRICS daga ranar Talata zuwa Alhamis a birnin Kazan na kasar Rasha, kwararru daga kasar Zambia sun bayyana cewa, tsarin BRICS ya zama muhimmin dandalin hadin kan kasashe masu saurin ci gaban tattalin arziki da samun saukin shiga harkokin cinikayyar duniya.
Mwaka Chikoye, wani mai bincike kuma jigo a kungiyar huldar kasa da kasa ta kasar Zambia, ya bayyana cewa, kasashen da ke cikin tsarin BRICS na da kima musamman ga kasashen da ke da muradun bai daya, musamman a yayin da ake samun karuwar kariyar cinikayya a duniya. Ya shaida wa manema labaru cewa, tsarin hadin gwiwa na BRICS yana da matukar muhimmanci, musamman ga kasashe masu saurin ci gaban tattalin arziki. Ya yi imanin wannan tsari zai samar da wani dandali ga kasashe da za su karfafa hadin kai tare, don taimakawa wajen cimma moriyar juna.
Kazalika, Musonda Malupenga, wani mai bincike kuma mai ba da shawara kan harkokin yada labarai daga Zambia, ya amince da ra'ayin Chikoye, ya kuma yi nuni da cewa, tsarin BRICS ya samar da saukin gudanar da cinikayya a duniya ga kasashe masu tasowa. Ya yi nuni da cewa, tallafin bunkasa ababen more rayuwa da kasar Sin ta baiwa Zambia, yana matsayin abun shaida na fa'ida ta zahiri da BRICS ta samar. (Yahaya)