logo

HAUSA

Gwamnatin Najeriya: makaman da ake safarar su ba bisa ka’ida ba cikin kasar suna biyowa ne ta kasashen dake yankin kogin Guinea

2024-10-23 09:46:03 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara gudanar da bincike game da yadda ake amfani da kasashen dake yankin kogin Guinea wajen safarar makamai cikin kasar.

Babban mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribado ne ya bayyana hakan jiya Talata 22 ga wata a birnin Abuja yayin taron karawa juna sani na kwanaki biyu a game da sauyin yanayi da kuma yaduwar makamai da tabarbarewar tsaro a kasashen dake yankin kogin Guinea.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Taron wanda cibiyar dakile yaduwar kanana da manyan makamai ta kasa tare da hadin gwiwa da cibiyar sadarwa da ci gaban dan adam ta duniya suka shirya, ya mayar da hankali sosai a kan yadda za a kara sanya idanu a iyakokin kasashen dake shiyyar domin dai tabbatar da ganin an toshe duk wata kafa ta shigowa da makamai Najeriya ba tare da sanin hukumomi ba.

Malam Nuhu Ribadu ya ci gaba da cewa, kamar yadda bincike ya nuna irin wadannan mutane na amfani da jiragen ruwan da suke zirga-zirga a kogin wajen safarar kwaya da na bil`adama da satar mai da safarar muggan makamai da kayayyakin da aka haramta shigowa da su da kuma garkuwa da mutane, musamman ma dai direbobin jiragen ruwa na dakon kaya da ma’aikatansu. (Garba Abdullahi Bagwai)