logo

HAUSA

Kasar Sin za ta samar da kwararrun ’yan kwadago 62,000 nan da shekarar 2035

2024-10-22 14:54:22 CMG Hausa

Kasar Sin na da burin samar da ma’aikatan masana’antu a mataki mafi girma da nufin ba da taimakon hazaka da fasaha mai karfi don gina babbar kasa, da kuma sake farfado da al'ummar Sinawa ta hanyar zamanantar da kasar Sin.  

Ta hanyar zurfafa gyare-gyare a fannin gina ma’aikatan masana’antu, kasar na da niyyar samar da kwararrun ’yan kwadago kimanin 2,000 a matakin kasa, 10,000 a matakin larduna, da 50,000 a matakin birane, wadanda ke da ilimi sosai kuma masu basira da fasahohin kirkire-kikire nan da shekarar 2035, bisa ga ka’idojin da kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin da majalisar gudanarwar kasar suka fitar.

Don dacewa da bukatun sabbin masana’antu, kasar za ta habaka ilimin sana’o’in zamani, da kara kokarin habaka hazaka tare da cikakkiyar kwarewar fasaha, da kuma daidaita tsarin horar da sana’o’i na tsawon rayuwa ga ma’aikatan masana’antu, da nufin samar da gwanintar da ake bukata cikin gaggawa don bunkasa sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, da sa kaimi ga samar da ci gaba mai inganci, bisa ga ka’idojin. (Yahaya)