Hukumar kidayar jama’a a tarayyar Najeriya ta ce, adadin mutane 700,701 ne annobar ambaliya a Maiduguri ya shafa
2024-10-22 11:35:54 CMG Hausa
Hukumar kidayar jama’a a tarayyar Najeriya ta fitar da kidaddigar dake nuna cewa adadin mutane dubu dari bakwai da dari bakwai da daya ne ambaliyar ruwa a Maiduguri ya shafa, sannan kuma gine-gine dubu dari da ashirin da tara da dari tara ne suka lalace sakamakon annobar.
Shugaban hukumar Alhaji Nasir Isa Kwarra ne ya tabbatar da hakan lokacin da ya jagoranci manyan jami’an hukumar zuwa jihar Borno domin gabatar da jajen su ga gwamnatin jihar.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Shugabannin hukumar kidayar ta kasa dai sun sami ganawa da gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum yayin ziyarar, inda suka gabatar masa da kwafen kididdigar da aka gudanar game da asarar ambaliyar ruwan ya haifar.
Alhaji Nasir Isa Kwarra ya ce, kaso 55.8 na gine-ginen da ambaliyar ya shafa muhalli ne na kwanan jama’a yayin da kuma kaso 43.5 wuraren kasuwanci ne, har’ila yau kuma rahoton hukumar ya nuna cewa kaso 1.24 ne kawai na gaba daya gine-ginen da ruwan ya lalata suka kasance mallakin gwamnati, wanda ofishin hukumar kidayar jama’ar yana daya daga cikin gine-ginen. (Garba Abdullahi Bagwai)