Gwamnatin jihar Yobe za ta mika filin kiwon dabbobi na zamani da ta gina ga shugabannin Fulani dake jihar
2024-10-22 11:37:06 CMG Hausa
Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya umarci ma’aikatar gona da albarkatun kasa ta jihar da ta gaggauta mika cibiyar bunkasa kiwon dabbobi dake karamar hukumar Jakusko ga shugabannin Fulani na jihar.
Gwamnan ya bayar da umarnin ne jiya Litinin 21 ga wata cikin wata sanarwar da jami’ar yada labaran ma’aikatar gona ta jihar Aishatu Tijjani ta rabawa manema labarai a Damaturu, fadar gwamnatin jihar.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Gwamna Mai Mala Buni ya ce, daya daga cikin makasudin gina cibiyar bukasa kiwon dabbobin na Nazari dake karamar hukumar Jakusko shi ne tsugunar da Fulani makiyaya wurin guda domin su mayar da hankalinsu wajen sana’ar kiwo a zamanance tare kuma da samun damar sanya ’ya’yan su a makaranta.
Kayayyakin da aka samar a filin sun hada da cibiyar adana madara, da makarantar firamare domin ’ya’yan makiyaya da wuraren shayar da dabbobi da asibitin dabbobin da kuma na lura da makiyaya da iyalansu. (Garba Abdullahi Bagwai)