logo

HAUSA

Hukumomin birnin Yamai sun dukufa wajen yaki da matsalar fashi da makami

2024-10-20 14:48:04 CMG Hausa

A jamhuriyyar Nijar, a ranar jiya Asabar 19 ga watan Oktoban shekarar 2024, babban ma’aikatar ’yan sanda na PJ cewa da Police Judiciaire, suka gabatar wa ’yan kasar Nijar da kuma ’yan jarida da wani gungun ’yan daba dake fashi da makami a birnin Yamai.

Daga birnin Yamai, abokin aikimu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

Shi dai wannan gungun ’yan fashi da makami da dubunsu ta cika ya kunshe mutum 9 dukansu maza dake da mabambantan shekaru tsakanin shekara 25 zuwa shekara 35. Daga cikin wadannan mutane 9 da ’yan sanda suka kama, akwai ’yan fashi 5 da masu sanyen kayan sata su sai da mutum 4.

Sace-sacensu da fashi da makaminsu na baya bayan nan sun bayyana a yayin da kyamarori suka nadi bidiyonsu a lokacin da suke ma mutane fashi da makami a cikin wasu unguwanni na birnin Yamai.

Bidiyoyin da suka yi yawo kan shaffukan sada zumunta na Wazap da Facebook, tare da janyo farga da tsoro ga zukatan mazauna birnin Yamai, musamman mata, da barayin suka fi kai ma hari da adduna da bindiga.

Mazauna birnin Yamai da dama ne, wadannan barayi da ’yan fashi da makami suka jikkata, tare da karbe musu kudi da salula da kayayyaki masu daraja.

A lokacin ’yan sanda suka kai samame da bincike a gidajensu, hakan ya taimaka wajen sanya hannu kan kayayyaki da dama da suka hada da wayoyin salula 114, allon salula 5, kwamfuta 4, da monita 1.

Daga karshe babban ofishin ’yan sanda na PJ ya gargadi jama’a da suka hattara, da nuna godiya ga ’yan kasa bisa ga taimakon da suka bada wajen kama wadannan miyagun mutane dake hadabar mazauna birnin Yamai da kuma gurbata kwanciyar hankali.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.