Xi ya jaddada bukatar ingiza bude kofa a matsayin koli domin cimma nasarar sauye sauye da samar da ci gaba
2024-10-20 19:55:13 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga yankunan bunkasa tattalin arziki, da na bunkasa fasahohi dake matakin kasa, da su ci gaba da ingiza karsashin kirkire kirkire, da habaka saurin samar da nasarori, da yayata bude kofa a matsayin koli, don cimma nasarar zurfafa sauye sauye, da bunkasuwa a matakin koli.
Shugaba Xi, ya yi tsokacin ne a baya bayan nan, cikin wani umarni da ya bayar, don gane da ayyukan wadannan yankuna na bunkasa ci gaban kasar Sin. (Saminu Alhassan)