logo

HAUSA

Sin a shirye take ta yi hadin gwiwa da sauran kasashe a fannin kare ikon mallakar fasaha

2024-10-20 21:22:02 CMG Hausa

Mataimakin firaministan kasar Sin Zhang Guoqing, ya ce Sin a shirye take, ta yi karin hadin gwiwa mai ma’ana, da cimma moriya tare da sauran kasashe a fannin kare ikon mallakar fasaha, ta yadda hakan zai amfani karin kasashe da al’ummun su.

Zhang ya bayyana hakan ne jiya Asabar, cikin jawabin da ya gabatar yayin bikin bude dandalin kasa da kasa na kungiyar kare ikon mallakar fasaha na shekarar nan ta 2024.  (Saminu Alhassan)