Kamfanin Huawei ya kaddamar da gasar fasahar sadarwa ta farko a Kenya
2024-10-18 11:09:24 CMG Hausa
Kamfanin sadarwa na Huawei na kasar Sin ya kaddamar da gasar fasahar sadarwa ta shekarar 2024-2025 da wani shiri a jami’ar Nairobi, wadda ita ce mafi dadewa a kasar Kenya.
A cewar kamfanin Huawei, shirin na farko wanda ya ja hankalin dalibai sama da 250, babbar nasara ce dake nuna karuwar sha’awar ilimin fasahar sadarwa da kirkire-kirkire a fadin Kenya.
Daraktan cibiyar raya fasahar sadarwa ta jami’ar Nairobi Paul Kariuki, ya ce gasar wata dama ce ga dalibai ta inganta kwarewarsu da gano sabbin ci gaban da aka samu a bangarori kamar na tsarin hidimomin kwamfuta na Cloud da kirkirarriyar basira wato AI da harkokin sadarwa.
Shirin zai ci gaba da gudana a sauran jami’o’in kasar Kenya, ciki har da Jami’ar Zetech da jami’ar Kenyatta da ta Multimedia da ta Embu da kuma jami’ar Dedan Kimathi.
Mashirya gasar na da burin ganin mutane sama da 7,000 sun shiga an dama da su, inda za ta zama gasa mafi girma ta fasahar sadarwa ga daliban kasar Kenya. (Fa’iza Mustapha)