logo

HAUSA

Firaministan kasar Sin ya jagoranci taron majalisar gudanarwar kasar Sin

2024-10-18 20:58:01 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang ya jagoranci taron majalisar gudanawar kasar Sin a yau Juma’a, inda aka tattauna tare da samar da matakan kafa kasuwar kasa ta bai daya.

A cewar taron, gina kasuwar bai daya ta kasa na da nufin samar da ingantacciyar hanyar kasuwanci cikin daidaito da tsari, inda ya yi kira da hadewar muhimman dokokin kasuwa, da ka’idojin kasuwa na bai daya cikin daidaito, da kuma hadewar ababen more rayuwa na kasuwa mai inganci. (Yahaya)