Wang Yi ya yi kira ga hadin gwiwar Sin da Amurka don tinkarar kalubalen duniya
2024-10-18 20:22:15 CMG Hausa
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana a yau Juma’a yayin ganawarsa da shugaban kamfanin ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Amurka cewa, ya kamata kasashen Sin da Amurka su sauke nauyin da ke wuyansu na manyan kasashen duniya wajen tinkarar kalubalolin da duniya ke fuskanta, domin cimma nasara tare.
A yayin ganawarsa da shugaban kamfanin Eurasia Ian Bremmer, Wang ya jaddada cewa, wannan shi ne muradun al’ummonin kasashen biyu, kuma shi ne fatan al’ummomin duniya baki daya.
A nasa bangare kuwa, Bremmer ya bayyana farin cikinsa ganin yadda alakar Sin da Amurka ta nuna alamun kwanciyar hankali saboda kokarin da bangarorin biyu suka yi, tare da nuna aniyarsa ta ci gaba da ba da shawarwari na gaskiya domin dorewar zaman lafiya a tsakanin kasashen biyu. (Yahaya)