logo

HAUSA

Shugaba Xi ya yi rangadi a birnin Zhangzhou na lardin Fujian

2024-10-16 14:33:12 CMG Hausa

Da tsakar ranar jiya Talata ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya kai ziyara kauyen Aojiao na garin Chencheng, da dakin tunawa da marigayi Gu Wenchang, da yankin masana’antu na raya al’adu na Guandi dake gundumar Dongshan ta birnin Zhangzhou a lardin Fujian.

Shugaba Xi ya yi amfani da ziyarar wajen fahimtar yadda ake ingiza cikakken shirin farfado da kauyuka, da ruhun ci gaban jam’iyyar kwaminis ta Sin, da karfafa tsarin kare al’adu da aka gada daga kaka da kakanni. (Saminu Alhassan)