Bankin Duniya: Wajibi ne Najeriya ta tabbatar da dorewar sauye-sauyenta a fagen tattalin arziki har zuwa shekaru 10 zuwa 15
2024-10-16 09:22:02 CMG Hausa
Bankin duniya ya ce, wajibi ne Najeriya ta ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen da take yi a fagen tattalin arziki har zuwa nan da shekeru 10 zuwa 15 kafin ta fara ganin daidaituwar al’amura.
Babban mataimakin shugaban gungun cibiyoyin samar da ci gaba dake da hadaka da bankin Mr. Indermit Gill ne ya bayyana hakan ranar Litinin da ta gabata lokacin da yake gabatar da jawabinsa yayin babban taron kasa karo na 30 kan tattalin arziki a birnin Abuja.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Mr Indermit Gill ya ce, sauye-sauyen da ake yi a halin yanzu yana da matukar muhimmanci domin samun ci gaba mai dorewa, ta yadda Najeriya za ta kai ga yin gogaiya da kasashen dake nahiyar Afrika da ma duniya da yanzu haka tattalin arzikinsu ke bunkasuwa.
Mr Indermit ya ci gaba da cewa, hakika matakan sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Najeriya ke kan gudanarwa yanzu muddin aka ci gaba zai iya maido da naira tiriliyon 10 da aka barnatar da ita lokacin da ake bayar da tallafin man fetur da kuma kudin da aka kashe yayin musayar kudaden waje.
Ya ce, gyaran tattain arzikin kasa, yana da matukar wahalar gaske, amma dai ribarsa tana da yawa sosai, inda ya bukaci ’yan Najeriya da su kara nuna juriya tare da marawa kokarin gwamnati baya domin cimma burin da ake son cimmawa. (Garba Abdullahi Bagwai)