Hukumomin Nijar sun yi odar jiragen saman soja masu tuka kansu guda 5 daga Turkiya
2024-10-15 10:02:44 CMG Hausa
A jamhuriyyar Nijar, a wani labarin da ya fito a ranar jiya Litinin 14 na nuna cewa hukumomin soja na kwamitin ceton kasa CNSP da shugaban Abdourahamane Tiani yake jagoranta sun cimma wata yarjejeniya sayen jiragen sama na soja masu tuka kansu daga kasar Turkiya.
Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
Mujallar labarun sojoji ta kasar Nijar cewa da “Infos Militaires-IM” a fitowarta ta ranar jiya Litinin 14 ga watan Oktoban shekarar 2024, ta ba da labarin cewa kasar Nijar ta sanya hannu kan yin odar jiragen saman soja masu sarrafa kansu guda biyar daga kasar Turkiya na jimillar kudin da suka tashi zuwa dalar Amurka miliyan 80.
Samun kayayyakin musamman da aka cimma tare da kamfanin kera makaman yaki na kasar Turkiya Vestel Defens da ya kunshi sayen wani gungun jiragen sama na soja masu sarrafa kansu samfurin Karayel-SU.
Wadannan jirage na yaki masu tuka kansu, a cewar wannan mujallar soja suna iyar aiki a cikin dukkan yanayi na ruwa ko iska, ko kura, da kuma karfin tantance abubuwa masu motsi da kuma wadanda ba su motsi, da kuma cimma wani gudu na kilomita 148 a duk awa guda.
Haka kuma wadannan jiragen masa na soja masu sarrafa kansu suna iyar daukar boma-bomai 12 kirar MAM-S.
Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar. (Mamane Ada)