logo

HAUSA

Shugaban Masar ya bukaci daukar matakan siyasa da hadin gwiwa don tabbatar da cin gajiyar albarkatun ruwa

2024-10-14 12:31:28 CMG Hausa

Shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi, ya bukaci daukar matakan siyasa, da aiki tukuru, da hadin gwiwa tsakanin kasashe masu ruwa da tsaki a batun kogin Nilu, don tabbatar da cin gajiyar albarkatun ruwa.

Shugaba Al-Sisi ya yi kiran ne a jiya Lahadi, cikin wani sakon bidiyo da aka nada, wanda aka gabatar yayin taro na 7 na makon ruwa da aka bude a birnin Alkahira. Ya ce kogin Nilu na samar da sama da kaso 98 bisa dari na yawan ruwan da Masar ke amfani da shi, don haka ya zama tushen rayuwa, da wanzuwar ta ga al’ummar Masar.

To sai dai kuma a cewar sa, Masar, da Sudan, da habasha sun shafe tsawon shekaru suna tattaunawa game da tsarin aiki, da batun doka mai nasaba da shigar da ruwa cikin madatsar ruwan nan ta GERD, wadda Habasha ta gina kan kogin na Nilu.

Habasha ta fara gina madatsar ruwa ta GERD ne a shekarar 2011, inda ake sa ran za ta rika samar da wutar lantarki da ta kai sama da megawatt 6,000 daga gare ta, yayin da kasashen Masar da Sudan ke nuna damuwa, don gane da yadda dam din zai rage musu yawan ruwan da suke samu daga kogin na Nilu.  (Saminu Alhassan)