logo

HAUSA

Xi: Sin a shirye take ta yi aiki tare da Indonesia wajen inganta hadin gwiwar shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”

2024-10-14 20:51:13 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yau Litinin cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasar Indonesia wajen inganta hadin gwiwarsu a bangaren shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”, da tabbatar da dorewar aikin layin dogo na jirgin kasa mai saurin tafiya na Jakarta da Bandung, da kyautata hadin gwiwa don kara amfanar jama'ar kasashen biyu.

Xi ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban kasar Indonesia Joko Widodo. (Yahaya)