’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane da dama a hanyar Gusau zuwa Zamfara
2024-10-14 10:21:55 CMG Hausa
Barayi masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da matafiya da dama a kan hanyar Gusau zuwa Funtua a ranar Asabar 12 ga wata.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Zamfara ASP Yazid Abubakar ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai jiya Lahadi 13 ga wata, ya ce, har kawo wannan rana ta Litinin ba a kai ga tantance adadin wadanda aka yi garkuwa da su din ba.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Kakakin rundunar ’yan sandan ya ce ’yan bindigar dai sun tsaya ne a daidai kauyen Kucheri zuwa Magazu dake babbar hanyar Funtua zuwa Tsafe a jihar Zamfara da yammacin ranar Asabar da ta gabata, inda suka yi ta harbin motoci barkatai da suke dauke da fasinjoji.
Ya ce a halin da ake ciki dai hadin gwiwar jami’an tsaro tare da ’yan sanda suna kan aikin ceton mutanen da aka yi garkuwa da su.
Sai dai ASP Yazid Abubakar ya musanta rahotannin da ake yadawa cewa wai masu garkuwa da mutanen sun kashe ’yan sanda biyar yayin musayar wuta a tsakaninsu.
A wani rahoton da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya bayyana kudurin gwamnatin jihar na tallafawa iyalan dakarun tsaron sa kai da suka rasa rayukansu a lokacin da suke tsaka da yaki da ’yan bindiga a sassan jihar daban daban.
Sanarwar ta bayyana cewa gwamnan jihar Alhaji Dauda Lawan ya tabbatar da hakan ne ranar Asaabr 12 ga wata lokacin da ya ziyarci masarautar Tsafe domin dai gabatar da jajensa ga iyalan dakarun sa kai su 9 da ’yan bindiga suka kashe a farkon makon da ya gabata.
Gwamnan ya ce, duk da koma bayan da ake samu kan sha’anin tsaro a kwanan nan a jihar ta Zamfara, amma wannan ba zai hana gwamnati ci gaba da daukar managartan matakai da za su kawo karshen ayyukan ’yan bindiga ba a jihar. (Garba Abdullahi Bagwai)