logo

HAUSA

OCHA ya ce adadin mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a yammaci da tsakiyar nahiyar Afirka ya kai miliyan 6.6

2024-10-12 17:34:59 CMG Hausa

Ofishin hukumar kula da ayyukan jin kai na MDD ko OCHA, ya ce adadin mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a yankunan yammaci da tsakiyar nahiyar Afirka na ta karuwa, inda ya zuwa yanzu ya kai mutum miliyan 6.6 a kasashe 16.

OCHA ya ce kasashen da suka fi fuskantar mummunan tasirin ambaliyar a bana sun hada da Chadi, inda ambaliyar ta shafi mutane miliyan 1.9, sai Jamhuriyar Nijar da mutane miliyan 1.3, da Najeriya mai mutum miliyan 1.2, yayin da ambaliyar ruwan ta shafi mutane miliyan 1.1 a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.

Kaza lika a cewar ofishin, ya zuwa makon jiya, kawancen masu samar da tallafin jin kai da hukumomi, sun ce sama da mutane 1,400 sun rasu, baya ga wasu 980,000 da suka rasa matsugunan su sakamakon ibtila’in.

Har ila yau, ambaliyar ruwan ta lalata hekta 700,000 ta gonaki, ta kuma hallaka sama da shanu 120,000, lamarin da ya kara tsananta matsalar kamfar abinci, da abinci mai gina jiki da ake fuskanta a yankin.

OCHA ta kuma ce MDD, da sauran abokan huldar samar da agajin jin kai na ci gaba da tallafawa kokarin da ake yi na samar da taimako, ciki har da samar da abinci, da ruwan sha mai tsafta, da kudade agaji, da abubuwan tsafta, da tallafin matsugunai da na kayan kiwon lafiya a yankin. (Saminu Alhassan)