Xi Jinping ya aika da sakon taya murna ga sabon shugaban kasar Habasha
2024-10-12 18:44:21 CMG Hausa
Yau Asabar 12 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aika da sako ga Taye Atske-Selassie Amde, domin taya shi murnar sha rantsuwar shugabancin kasar Habasha.
Xi Jinping ya nuna cewa, yana mayar da hankali sosai kan raya dangantakar dake tsakanin Sin da Habasha, yana kuma fatan yin aiki tare da shugaba Taye, don yin amfani da damar tabbatar da sakamakon da aka cimma a gun taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka na shekarar 2024 da aka gudanar a Beijing, wajen sa kaimi ga kara samun sabbin nasarori, a dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a duk wane halin da ake ciki tsakanin Sin da Habasha, da ma haifar da alfanu ga jama’ar kasashen biyu. (Bilkisu Xin)