logo

HAUSA

Wang Yi ya halarci taron sada zumunta tsakanin Sin da sassan ketare

2024-10-12 19:06:14 CMG Hausa

A yau Asabar a nan birnin Beijing, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya halarci liyafar maraba da mahalarta taron sada zumunta tsakanin Sin da ketare, kana bikin murnar cika shekaru 70 da kafuwar kungiyar sada zumunta tsakanin Sin da sassan ketare, tare da ba da jawabi.

A jawabinsa, Wang Yi ya jaddada cewa, kasarsa na maraba da karin masu idon basira na kasa da kasa, da su himmatu wajen tabbatar da sada zumunta tsakanin al’ummomi, don ba da gudummawarsu wajen gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga dukkanin bil’adama.   (Bilkisu Xin)