Za a kone gawar marigayi tsohon shugaban majalisar dokokin kasar Sin Wu Bangguo a ranar Litinin
2024-10-12 15:57:01 CMG Hausa
Mahukuntan kasar Sin sun sanar da shirin kone gawar marigayi tsohon shugaban majalisar dokokin kasar Sin, Wu Bangguo, a ranar Litinin 14 ga watan nan a birnin Beijing.
Wu Bangguo, tsohon shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ko NPC, ya rasu ne a ranar Talata 8 ga wata a birnin Beijing, bayan ya yi fama da rashin lafiya. Ya rasu yana da shekaru 84 a duniya.
Domin makokin tsohon jami’in, a ranar Litinin, za a sassauto da tutar kasar Sin zuwa rabin sanda, a filin taron jama’a na Tiananmen, da na Xinhuamen, da babban dakin taruwar jama’a, da ma’aikatar harkokin wajen Sin dake Beijing, da ofisoshin kwamitocin JKS, da na gwamnatocin larduna.
Sauran wuraren sun hada da ofisoshin gwamnatocin jihohi masu cin gashin kai, da manyan biranen kasar Sin, da yankin musamman na Hong Kong, da Macao, da kan iyakokin kasa, da tashoshin ruwa, da filayen jiragen sama na shigowa kasar, da manya da kananan ofishoshin jakadancin kasar Sin dake kasashen waje. (Saminu Alhassan)