Afirka na asarar dalar Amurka biliyan 4.2 a duk shekara a dalilin yada labaran son zuciya da kafafen yada labarai na yamma ke yi
2024-10-11 10:15:02 CMG Hausa

Wani binciken da aka kaddamar a jiya Alhamis ya nuna cewa, yadda kafafen yada labarai na kasashen yammacin duniya ke yada munanan labarai kan al’amuran Afirka, na hana tattalin arzikin nahiyar samun dala biliyan 4.2 a duk shekara.
Binciken wanda kamfanin Africa Practice, wani kamfani mai ba da shawarwari da dabaru, da Africa No Filter, wata kungiya mai fafutukar kare hakkin jama’a suka gudanar, ya dora laifin kan yadda kafafen yada labarai na yammacin duniya ke yada munanan labarai game da nahiyar wanda ke kashe gwiwar masu zuba jari da gurgunta ci gaban tattalin arzikin nahiyar.
Binciken mai taken "Illar yada munanan labarai game da Afirka" ya mayar da hankali ne kan tsarin zabe a Kenya, Najeriya, Afirka ta Kudu da Masar, da kuma yadda kafafen yada labaran kasashen suka ci gaba ke yada munanan labarai game da Afirka.
Binciken ya ce,"Kafafen watsa labaru na mai da hankali kan kasashen Afirka a lokutan zabe, amma su kan karkata hankalin nasu kan batutuwa marasa kyau kamar tashin hankali da magudin zabe."
Ya bayyana cewa, kasashen da ba na Afirka ba, wadanda ke da irin wannan hadari a lokutan yakin neman zabe, kafafen yada labarai na yammacin duniya sun fi nuna mafi kyawun al’amura game da su, inda ya kara da cewa, nahiyar Afirka za ta iya adana kusan kashi 0.14 cikin dari na GDPnta a duk shekara, bisa la’akari da kyakkyawar ra’ayoyin kafofin watsa labarai. (Mohammed Yahaya)
