logo

HAUSA

Sin ta sha alwashin shiga a dama da ita wajen yayata ka’idojin nan 5 na wanzar da zaman lafiya in ji firaminista Li Qiang

2024-10-11 20:38:39 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce Sin a shirye take ta yi aiki da dukkanin sassa, wajen yayata ka’idojin nan 5 na wanzar da zaman lafiya, da mayar da hankali wajen gina al’ummar duniya mai makomar bai daya.

Li ya bayyana hakan ne a Jumma’ar nan, yayin da yake jawabi gaban mahalarta taron kasashen gabashin Asiya karo na 19, a birnin Vientiane, fadar mulkin kasar Laos.

Firaministan na Sin ya kuma yi kira ga daukacin sassa da su goyi bayan matakan wanzar da zaman lafiya da lumana, da neman cimma moriyar juna, da sakamakon da zai amfani kowa, kana da rungumar matakan ingiza kara bude kofa da hadin gwiwa.

Daga nan sai ya yi kira ga kasashen da batun ya shafa dake wajen yankin, da su martaba, da goya baya ga kokarin Sin na yin hadin gwiwa da kasashen, wajen kare zaman lafiya da daidaito a tekun kudancin Sin, da taka rawar da ta dace wajen gina zaman lafiya da daidaito a yankin baki daya. (Saminu Alhassan)