logo

HAUSA

Xi Jinping ya taya Kais Saied murnar sake lashe babban zaben kasar Tunisiya

2024-10-10 10:44:16 CMG Hausa

Jiya Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya buga wa shugaban kasar Tunisiya Kais Saied waya, domin taya shi murnar sake lashe babban zaben Jamhuriyyar kasar Tunisiya.

Xi Jinping ya ce, kasar Sin da kasar Tunisiya na da zumunci mai zurfi. A ‘yan shekarun nan, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu na bunkasa yadda ya kamata bisa jagorancin shugabannin kasashen biyu, kana, an cimma sakamako da dama bisa hadin gwiwa da mu’amalar dake tsakaninsu.

Haka kuma, ya ce, yana mai da matukar hankali wajen raya dangantakar dake tsakanin Sin da Tunisiya. Kana, yayin da bana ke cika shekaru 60 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Tunisiya, Xi Jinping ya ce, a shirye yake ya yi aiki da shugaba Saied wajen ci gaba da zurfafa zumunci da hadin gwiwa dake tsakanin kasashen biyu, tare da inganta dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu. (Mai Fassara: Maryam Yang)