logo

HAUSA

Yawan kwangilolin da kamfanonin kera jiragen ruwa dake aiki da makamashi mai tsabta na Sin suka samu ya kai kashi 70% bisa na duniya

2024-10-10 11:17:54 CMG Hausa

 

Yau Alhamis, hukumar masana’antu da sadarwa ta kasar Sin ta gabatar da sabon alkaluma kan sana’ar kera jiragen ruwa na watan Janairu zuwa Satumba na bana.

Bisa alkaluman da hukumar ta bayar, a wadannan watanni, yawan nauyin sabbin jiragen ruwa da aka kera wato yawan GDWT ya kai ton miliyan 36.34, wanda ya karu da kashi 18.2% bisa na makamancin lokacin bara. Yawan GDWT na sabbin kwangilolin da aka samu ya kai ton miliyan 87.11, wanda ya karu da kashi 51.9% bisa na makamancin lokacin bara. Ya zuwa karshe watan Satumba, yawan GDWT na jiragen ruwa da Sin take ginawa ya kai ton miliyan 193.3, wanda ya karu da kashi 44.3%. Ban da wannan kuma, daga watan Janairu zuwa Satumba, yawan GDWT na muhimman ma’aunoni uku a bangaren kera jiragen ruwa na duniya ya kai kashi 55.1% da 74.7% da kuma 61.4% bisa na duniya.

Kazalika, yawan kwangilolin da kamfanonin kera jiragen ruwa dake aiki da makamashi mai tsabta na Sin suka samu ya kai kashi 70% bisa na duniya. An ce, kasar Sin ta samu sabbin kwangilolin kera 14 daga cikin muhimman nau’o’in jiragen ruwa 18 na duniya, lamarin da ya kai kasar Sin matsayin koli a duniya. Abubuwa 3 dake ba da muhimmanci a sana’ar kera jirgin ruwa na Sin su ne amfani da makamashi mai tsabta, da karin amfanin hajoji da ma fasahar kere-kere da kanta. (Amina Xu)