Burkina Faso: Hukumar sadarwa ta CSC ta dakatar VOA bisa tsawon watanni uku
2024-10-08 10:27:29 CMG Hausa
A kasar Burkina Faso, babbar hukumar dake kula da daidaita harkokin sadarwa ta kasa CSC, ta fitar da wata sanarwa a ranar jiya Litinin 7 ga watan Oktoban shekarar 2024 da matakin dakatar da watsa shirye-shiryen rediyon muryar Amurka bisa tsawon watanni uku.
Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
A cikin wata sanarwa ce ta hanyar gidan rediyo da talabijin na kasar Burkina Faso, babbar hukumar sadarwa ta kasa CSC ta bayyana babban dalilin daukar wannan mataki kan muryar Amurka VOA, shi ne game da shirin da aka watsa dake da manufar karya lagon rundunonin sojojin kasar Burkina Faso da na Mali a cikin wani dandalin muhawara mai sunan “Washington Forum” na ranar 19 ga watan Satumban shekarar 2024, da aka maimaita shirin ta gidan rediyo Ouaga FM mai zaman kansa.
Haka, kuma hukumar dake kula da daidaita labarai ta CSC ta yi wa rediyo Ouaga FM mai zaman kansa hannunsa mai sanda tare da yi masa kashedi game da nauyin da ya rataya kan wuyansa, da kuma kiransa ga yin hattara da yin taka tsatsan da kuma nemansa wajen nuna sanin ya kamata wajen zaben shirye-shiryen da ya kamata ya watsa.
Haka kuma, hukumar CSC ta hana da dukkan kafofin sadarwa na kasa watsa shirye-shiryen wani gidan rediyon waje.
A cikin watan Afrilun da ya gabata ne, hukumar ta CSC ta taba dakatar da VOA a tsawon makwanni biyu bisa zargin wannan kafar kasar Amurka da rawaito wani rahoton kungiyar HRW dake zargin rundunar sojojin kasar Burkina Faso da aikata kisan kiyashi kan fararen hulla.
Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.