logo

HAUSA

Nijar : Bankin duniya ya sanar da wani adadin raguwar talauci

2024-10-07 15:26:20 CMG Hausa

A ranar Lahadi 6 ga wata, a cikin wani rahoton da bankin duniya ya fitar ya yaba da kokarin huhukmomin kasar Nijar. Bankin duniya ya nuna cewa talauci ya ragu daga kashi 52% zuwa kashi 42.5%.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya hada mana wannan rahoto.

Shi dai wannan bayani na bankin duniya ko Bretton Woods ya nuna wani hasashen raguwa mai ban mamaki ta talauci a kasar Nijar. 

Alkaluman sun nuna cewa adadin talauci zai koma daga kashi 52 cikin 100 a shekarar 2023 zuwa kashi 42.5 cikin 100 nan da shekarar 2026, a cewar hasashen wannan hukumar kudi ta duniya.

Masanan tattalin arziki da dama ne suke ganin wannan hasashe, wani ci gaba ne ga kasar Nijar, da aka yi tsammanin kasar za ta fada cikin wani hali na koma baya bayan juyin mulki, da kuma biyo bayan yanke huldar dangantaka tare da wasu abokan hulda, tare da kasar Faransa da kuma kungiyar CEDEAO ko ECOWAS.

A cewar bankin duniya, wannan ci gaba abin yabo ne ga wannan kasa da ke shiyyar yammacin Afrika, ganin yadda kasar ta shiga wani lokaci na rigingimun siyasa.

A shekarar 2023, kasar Nijar ta kai wani mizalin karuwar talauci, da ya shafi mutane miliyan 14.1 sabanin mutane miliyan 1.1 a shekarar 2024.

A cewar bankin duniya, dage takunkumi a cikin watan Febrairun shekarar 2024, da kuma mai do da huldar dangantaka da abokan hulda ya taimaka wajen zaburar da tattalin arziki wannan kasa.

Bankin duniya ya yi hasashen wani karuwar tattalin arziki da kashi 5.7 cikin 100 a shekarar 2024, sabanin kashi 2 cikin 100 a shekarar bara.

Sai dai kuma duk da hasashen bankin duniya, a nasa bangaren bankin FMI ya yi hasashen ta bunkasuwa a kasar Nijar da kashi 10.6 cikin 100 a wannan shekara.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.