logo

HAUSA

Ana shirin jigilar fasinjoji fiye da miliyan 18 ta jiragen kasa a kasar Sin a yau Lahadi

2024-10-06 16:23:45 CMG Hausa

A yau Lahadi an kusan kai wa karshen lokacin hutu na kwanaki 7 na bikin kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, saboda haka a garuruwa daban daban na kasar, an fara samun dimbin fasinjoji masu hawa jiragen kasa, da suke neman komawa gidajensu daga wuraren da suka yi ziyarar bude ido, inda ake sa ran jigilar fasinjoji 18,730,000 ta jiragen kasa a yau, lamarin da ya sa ake shirin fara aiki da karin jiragen kasa 1432. Kafin haka, a jiya Asabar, an yi jigilar fasinjoji kimanin 17,881,000 ta jiragen kasa a kasar Sin.

An ce, yawan zirga-zirgar mutane a lokacin hutun bikin kafuwar kasa na wannan karo, ya sa yawan fasinjoji masu hawa jirgin kasa a kasar Sin ya zarce miliyan 17 a kowace rana, cikin kwanaki 6 a jere. Inda aka gudanar da aikin jigilar wadannan fasinjoji lami lafiya, ba tare da wata matsala ba. (Bello Wang)