Yawan jigilar kayayyaki a farkon watanni takwas na bana a Sin ya karu da kaso 5.4%
2024-10-05 15:59:14 CMG Hausa
Kungiyar jigilar kayayyaki da sayayya ta kasar Sin, ta fitar da alkaluman gudanar da ayyukan jigilar kayayyaki daga watan Janairu zuwa Agusta na bana a yau Asabar. Bayanan sun nuna cewa, yawan jigilar kayayyaki a zamantakewar Sinawa ya karu da kashi 5.4 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara.
Dangane da yawan jigilar kayayyakin masana'antu a watan na Agusta kuwa, samfuran fasaha kamar mutum-mutumin inji na masana'antu, da hadadden alluna laturori ko IC, sun ci gaba da habaka cikin sauri, kuma saurin bunkasar su ya kai kusan kashi 20 cikin dari.
Dangane da yadda ake cin gajiyar hakan, yawan jigilar kayayyakin kamfanoni, da na al’ummar kasar a farkon watanni takwas na bana ya karu da kashi 7.8 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara. A cikin wannan adadi kuma, bukatar jigilar kayayyakin ta yanar gizo ta fi saurin habaka, fiye da ta jigilar kayayyakin sayarwa na zahiri.
Dangane da fannin shige da fice kuwa, daga watan Janairu zuwa Agusta, jimillar yawan jigilar kayayyakin da ke shigowa ta karu da kashi 4.3 cikin dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, yayin da jimillar yawan jigilar kayayyakin da ake fitarwa ta karu da kashi 5 cikin dari, bisa na makamancin lokacin bara.
Dangane da masana'antu, a watan Agusta, jimillar yawan jigilar kayayyakin masana'antar kera na'urorin lantarki, da na sadarwa, ta karu da kashi 11.4 cikin dari, idan aka kwatanta da makamancin lokaci na bara, wanda hakan ya taimaka wajen habaka bunkasuwa a bangarorin masana'antu, da kasuwanci, da sauran fannoni. (Safiyah Ma)