logo

HAUSA

ECOWAS na shirin samar da rundunar tsaron hadin gwiwa da zata kula da harkokin tsaro a mambobin kasashe

2024-10-04 14:45:59 CMG Hausa

Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS na shirye- shiryen samar da dakarun tsaron hadin gwiwa dubu 5 da za su tunkari ayyukan ta'addanci a shiyyar.

Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar Omar Touray ne ya tabbatar da hakan ranar Alhamis 3 ga wata a birnin Abuja yayin babban taron lacca na kasa da kasa da kamfanin dillacin labaru na Najeriya ya shirya .

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Kungiyar ta ECOWAS ta tabbatar da cewa a tsakanin watan Janairu zuwa Agustan wannan shekara ta 2024, an sami hare-haren ta'addanci har 1,605 a kasashen dake yammacin Afrika inda aka jikkata mutane kusan 6,956.

Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar ta ECOWAS, wanda ya sami wakilcin babban jami'in lura da harkokin tsaro, zaman lafiya da siyasa na hukumar, Mr. Isaac Armstrong, ya ce bincike ya tabbatar da cewa kasar Burkina Faso ta fuskanci hare-haren ta'addanci a tsakanin wadannan watanni har 611 inda aka samu mutane 3,810 sun jikkata, sai mai biye mata kuma ita ce kasar Mali da ta fuskanci hare-hare 546 inda mutane 1,424 suka jikkata, sai kuma Najeriya da ta fuskanci hare-hare 238 inda kuma aka sami mutane 905 sun jikkata, wasu kuma suka rasa rayukan su.

Haka kuma binciken ya nuna cewa a tsakanin watan Janairu zuwa Agustan wannan shekara, an sami hare-haren 'yan ta'adda har sau 153 a janhuriyar Nijar, inda aka sami mutane 676 sun jikkata, a janhuiyyar Benin kuma an sami rahoton hare-hare 44 wanda ya yi sanadin jikkatar mutane 66, yayin da kasar Togo kuma binciken kungiyar ta ECOWAS ya nuna cewa an sami hare-haren yan ta'adda har sau 13 wanda ya yi sanadiyar jikkatar mutane 75.

Sai dai kuma shugaban hukumar gudanarwar kungiyar ta ECOWAS ya ce samar da wannan rundunar tsaron musamman ba zai daukewa kowacce kasa dake kungiyar nauyin lura da harkokin tsaron cikin gidanta ba.(Garba Abdullahi Bagwai)