Shugabannin duniya sun mika sakon taya Sin murnar cika shekaru 75 da kafuwa
2024-10-04 15:50:18 CMG Hausa
Shugabannin kasashen duniya daban daban, sun mika sakwannin taya murna ga shugaban kasar Sin Xi Jinping, game da cikar kasar Sin shekaru 75 da kafuwa. Cikin shugabannin da suka taya Sin murna a baya bayan nan akwai na Faransa da Afirka ta kudu.
Cikin sakon da ya aike ga shugaba Xi, shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya ce kasarsa a shirye take ta wanzar da kyakkyawan ci gaban dangantaka dake tsakanin sassan biyu, da ingiza tattaunawa tsakanin bangaren Sin da na Turai, da neman cimma moriyar bai daya ta sassan biyu, da bunkasa zaman lafiya a duniya, da hada karfi wajen shawo kan kalubalolin wannan lokaci, kamar batun sauyin yanayi.
A nasa sakon kuwa, shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, ya ce kasarsa na fatan ci gaba da karfafa hadin gwiwa a dukkanin matakai tare da Sin, da taimakawa Sin din wajen taka rawar jagoranci a matakin kasa da kasa.
Har ila yau, shi ma shugaban kasar Pakistan Asif Ali Zardari, ya ce Sin za ta ci gaba da cimma manyan nasarori a fannin farfado da kan ta. A daya hannun kuma Pakistan za ta wanzar da matsayin ta na aminiyar kasar Sin, kana kawa ta kut da kut, kuma abokiyar hulda da Sin za ta iya dogaro da ita. (Saminu Alhassan)