logo

HAUSA

Adadin fasinjojin da suka yi tafiye-tafiye a jiragen kasa a Sin ya yi matukar karuwa

2024-10-03 15:28:45 CMG Hausa

Yawan fasinjoji a kasar Sin da suka yi tafiye-tafiye a jiragen kasa ya kai miliyan 21.45 a ranar Talata, wato ranar farko ta hutun mako guda na bikin zagayowar ranar kafa kasa.

Wannan shi ne adadi mafi yawa a tarihi na tafiye-tafiyen fasinja na yau da kullum na jiragen kasa, a cewar kamfanin layin dogo na kasar Sin a ranar Laraba, ya kuma yi hasashen adadin zai ragu zuwa miliyan 18.2 a ranar Laraba.

Ana sa ran tsarin layin dogon zai yi jigilar fasinja miliyan 175 a yayin zirga-zirgar lokacin hutu na kwanaki 10 daga ranar 29 ga watan Satumba zuwa 8 ga Oktoba. Masu yawon bude ido, da masu haduwa da iyali da dalibai suke haifar da karuwar zirga-zirgar.

Jimillar layin dogo da ke aiki a kasar Sin ya zarce kilomita 160,000 a watan Satumban shekarar 2024, inda aka kaddamar da wani sashe da ya hada birane biyu a lardin Guangdong na kudancin kasar Sin. (Yahaya)