Sin ta bukaci a hana ci gaban rikici a Gabas ta Tsakiya
2024-10-02 20:26:38 CMG Hausa
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana yau Laraba cewa, kasar Sin ta yi kira ga kasashen duniya, musamman ma manyan kasashe masu tasiri, da su kara taka rawa wajen hana ci gaban rikici a yankin Gabas ta Tsakiya.
A ranar 1 ga watan Oktoba agogon Beijing ne, Isra’ila ta kaddamar da farmaki ta kasa a kudancin Lebanon. Da sanyin safiyar ranar 2 ga watan Oktoba kuma, Iran ta kaddamar da harin soji kan Isra’ila.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin na nuna matukar damuwa kan tashe-tashen hankula a yankin Gabas ta Tsakiya, yana mai bayyana cewa, kasar Sin na adawa da keta 'yanci, da tsaro da mutuncin yankunan Lebanon, kuma tana adawa da matakan da ke kara ruruta wutar rikici da kuma kara tada zaune tsaye.
Kakakin ya kara da cewa, kasar Sin ta yi imanin cewa, ci gaba da gwabza yaki a zirin Gaza, shi ne ummul aba'isin wannan zagaye na tashe-tashen hakula a yankin Gabas ta Tsakiya, kuma ya kamata dukkan bangarorin su yi gaggawar tsagaita bude wuta kuma mai dorewa. (Yahaya)