logo

HAUSA

Yawan lantarki da makamashi mai tsafta ke samarwa a kasar Sin ya karu

2024-10-01 20:28:41 CMG Hausa

Hukumar samar da lantarki ta kasar Sin ta ce jimilar karfin lantarki da tashoshin samar da makamashi mai tsafta da aka kafa a kasar Sin suka samar, ciki har da makamashin iska da rana da na halittu, ta haura kilowatt biliyan 1.27, zuwa karshen watan Agusta.

Wannan adadi kuma, shi ya dauki kaso 40.7 na jimilar lantarkin da kasar ke samarwa.

A cikin watan Agusta, makamashin da ba na albarkatun man fetur ba, shi ya dauki kaso 40 na makamashin da aka yi amfani da shi a kasar. (Fa’iza Mustapha)