Najeriya ta ce a shirye take ta shiga cikin kungiyar BRICS da zarar ta kammala kimtsawa
2024-10-01 15:33:00 CMG Hausa
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce a shirye take ta shiga cikin kungiyar fitattun kasashe masu karfin arziki na BRICS da zarar lokacin yin hakan ya yi.
Ministan harkokin kasashen waje na Najeriya Ambasada Yusuf Tuggar ne ya tabbatar da hakan ranar 30 ga watan jiya na Satumba a Legas lokacin da ake zantawa da shi a wata tashar talabijin mai zaman kanta, ya ce gwamnati na nan na nazarin al'amura, kuma da zarar ta kammala za ta sanar da shigar kasar cikin wannan kungiyar a hukumance.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Ambasada Yusuf Tuggar ya tabbatar dacewa har kawo wannan lokaci , Najeriya ba ta kammala zartar da shawarar shiga knugiyar ba, amma kuma ta dauki batun shigar da mahimmancin gaske bisa la'akari da tasirin da kungiyar ke da shi ga sha'anin tattalin arzikin duniya, wanda a kowanne lokaci kasashe da dama ke nuna muradin shiga cikin ta.
Ministan yace batun yanzu ba, gwamnatin Najeriya ta nuna sha'awar shiga cikin jerin kasashen kungiyar ta BRICS, kuma kamar yadda alamu suka nuna nan bada jimawa ba zata bayyanawa duniya shigar ta cikin kungyiar.
Ya ce jinkirin da Najeriya ke yi wajen shiga kungiyar, yana da nasaba ne da sauye sauyen manufofi da gwamnati ke yi a cikin gida wadanda suka hadar da na tattalin arziki da sha'anin gudanuwar shugabanci, inda ya ce ana daf da kammalawa.
Ambasadar Yusuf Tuggar ya ci gaba da cewa Najeriya tana da alaka mai kyau ta diplomasiyya da harkokin tattalin arziki da kasashen dake cikin kungiyar ta BRICS musamman ma kasar China, a saboda haka shigar ta cikin kungiyar tamkar karawa gishiri miya ne.(Garba Abdullahi Bagwai)