logo

HAUSA

Sin ta karrama baki kwararru da lambar yabo ta abota

2024-10-01 15:24:52 CMG Hausa

Gwamnatin kasar Sin ta bayar da lambobin yabo na abota ga baki kwararru 100 dake aiki a kasar, domin jinjinawa gudunmuwarsu ga ci gaban kasar Sin.

Mambar majalisar gudanarwar kasar Shen Yiqin ce ta gabatar da lambobin yabon a jiya, inda ta lashi takobin kasar za ta samar da karin kyakkyawan yanayi da sauki ga bakin dake aiki da rayuwa a kasar Sin.

A cewarta, baki kwararru sun bayar da gagarumar gudunmuwa ga yunkurin Sin na zamanantar da kanta, kuma abu ne da al’ummar Sinawa ba za ta manta ba.

Ta kara da cewa, kasar Sin za ta inganta zamanantar da kanta da kara jan hankalin kwararru daga fadin duniya. Haka kuma za ta zurfafa gyare-gyare da ci gaba da inganta goyon bayan tsarin daukar baki aiki. (Fa’iza Mustapha)