Gwamnatin tarayyar Najeriya ta mika mototcin bas 64 masu aiki da iskar gas ga kungiyoyin kodagon kasar da na dalibai
2024-09-30 10:42:50 CMG Hausa
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta mika sama da motocin masu amfani da iskar gas na CNG 64 ga wakilan kungiyoyin kodago da kuma kungiyar daliban kasar.
Ministan kudi Mr. Wale Edun ne ya jagoranci wasu ministocin kasar a madadin gwamnatin tarayya wajen gabatar da motocin ranar Lahadi 29 ga wata a babban dakin taro na fadar shugaban kasa dake birnin Abuja, a wani bangaren da ci gaba da shagulgulan bikin cikar kasar shekaru 64 da samun ’yanci.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Da yake jawabi yayin gabatar da motocin, ministan kudin na tarayyar Najeriya ya ce, motocin dai za su taimaka daidai gwargwado wajen kawo sauki ga harkokin zirga-zirga.
Ministan kudin na tarayyar Najeriya ya ci gaba da cewa, gabatar da motoci 64 wani danba ne aka dora daga shirin da ake yi na samar da motocin bas masu amfani da iskar Gas na CNG sama da dari 5 da kuma masu amfani da wutar lantarki guda 100 a kasa baki daya. (Garba Abdullahi Bagwai)