logo

HAUSA

Amurka ce za ta yi fama da mummunan tasirin tallafin da take bayarwa ga neman ‘yancin Taiwan

2024-09-30 20:48:13 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce ‘yancin Taiwan abu ne mara yiwuwa, kuma nacewar da Amurka ke yi na taimakawa ‘yancin yankin da karfin tuwo, kanta zai koma, kuma za ta girbi abun da ta shuka.

Kakakin ma’aikatar Lin Jian ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai na yau Litinin, inda yake tsokaci game da sanarwar da fadar White House ta Amurka ta wallafa a shafinta na website cewa, kasar za ta samar da tallafin soji da darajarsa ta kai dala miliyan 567 ga yankin Taiwan na kasar Sin.

Lin Jian ya jaddada cewa, Sin na bukatar Amurka ta yi biyayya ga manufar kasar Sin daya tak a duniya har ma da sanarwoyi 3 dake tsakaninsu, kana ta daina samar da makamai ga Taiwan ta ko wacce hanya. Ya kara da cewa, duk yawan makaman da Amurka za ta samarwa Taiwan, ba zai sauya matsayin Sin na adawa da ‘yancin Taiwan da tabbatar da tsaron kasar da yankunanta ba. (Fa’iza Mustapha)