logo

HAUSA

An yi bikin kade-kade don murnar cika shekaru 75 da kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin

2024-09-30 19:27:38 CMG Hausa

An gudanar da bikin kade-kade a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing da yammacin jiya lahadi, domin murnar cika shekaru 75 da kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin.

Shugaba Xi Jinping da sauran shugabannin kasar ciki har da Li Qiang da Zhao Leji da Wang Huning da Cai Qi da Ding Xuexiang da Han Zheng da sauran manyan shugabanni da suka yi ritaya, na daga cikin mutane sama da 3,000 da suka halarci bikin.

A ranar 1 ga watan Oktoban ko wacce shekara ne ake bikin kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)