Shugaban kasar Sin ya lashi takobin samar da karin nasarori da zaman lafiya da ci gaban bil adama
2024-09-30 21:36:58 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce al’ummar Sinawa za ta samu karin manyan nasarori tare da bayar da gudunmuwa ga burin samun zaman lafiya da ci gaban bil adama.
Xi Jinping wanda kuma shi ne sakatare janar na kwamitin kolin JKS kuma shugaban kwamitin soja na tsakiya na kasar, ya bayyana haka ne yau Litinin, yayin wata liyafa da ta gudana a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing, domin murnar cika shekaru 75 da kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin.
A ranar 1 ga watan Oktoban ko wacce shekara ne ake bikin kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin.
A jawabinsa, a madadin kwamitin kolin JKS da majalisar gudanarwar kasar, ya mika gaisuwar girmamawa ga jama’ar dukkan kabilu dake kasar da manya da kanana jami’an rundunar sojin kasar da na rundunar ‘yan sanda da membobin sauran jam’iyyu da ma wadanda ba su da jam’iyya.
Har ila yau, ya mika gaisuwa ga jama’ar kasar dake yankunan musamman na Hong Kong da Macao da Taiwan da ma wadanda ke zaune a kasashen waje. Har ila yau, ya mika gaisuwa ga kasashe abokai da baki abokai wadanda suka damu da kasar tare da mara baya ga ci gabanta.
A cewarsa, a wannan sabon tafiya a sabon zamani, babban abun dake gaban JKS da gwamnatin kasar shi ne, gina kasar Sin zuwa kasa mai karfi da cimma farfadowarta a dukkan fannoni ta hanyar zamanantar da kanta. (Fa’iza Mustapha)